Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Hossein Amir-Abdollahian, ya ce an rubuta wasu bayanai game da abubuwan da aka amincewa, kuma bangaren Iran na dora muhimmanci kan hakan.
Kaza lika sauran sassa ma na maida hankali kan fannonin da aka tantance, da suka kunshi sassan da ake da sabani a kan su.
Jami’in ya kara da cewa, mataimakin shugaban ofishin tsara manufofi na tarayyar Turai EU Enrique Mora ya taka rawar gani wajen tsara tattaunawar da ta kai ga cimma matsayin na yanzu.
Ya ce sauran sassan dake cikin tattaunawar da suka hada da Faransa, da Birtaniya, da Sin da Rasha da Jamus, na maida hankali matuka ga tattaunawar, kuma abu ne mai yiwuwa a kai ga cimma yarjejeniya mai armashi a nan gaba.
342/